Skip to main content

Featured

SHIN KO KASAN WANI BABBA MAHIN MANCI ZOGALE A JIKIN KU

AMFANIN KUKA A JIKIN DAN ADAM GARIN KUKA YA KUNSHI ABUBUWA MASU GINA JIKI KAMAR. 1, Calories: 50 2, Protein: 1 gram 3, Carbohydrates: 16 grams 4, Fat: 0 grams 5, Fiber: 9 grams 6, Vitamin C: Kashi 58% na Amfanin Kullum (RDI) 7, Vitamin B6: 24% na RDI 8, Niacin: 20% na RDI 9, Iron: 9% na RDI 10, Potassium: 9% na RDI 11, Magnesium: 8% na RDI 12, Calcium: 7% na RDI Kuka bishiya ce mai asali da ake samu a nahiyar Afirka da kuma wani yanki na kasashen Larabawa. A al'adance bishiyar kuka tana da matsayi da muhimmanci ga abinci da magungunan mutanen Afirka. Kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya, kamar yadda mujallar lafiya ta Healthline ta bayyana a wani bincikenta game da amfanin kuka ga lafiyar dan Adam. Tun daga daga ganyen kuka da ɓawon da Ę“aĘ“an kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum. Mujallar ta ce kuka tana ʙunshe da kusan dukkanin sinadaran da jikin mutum yake buʙata - Kuka na da sinadarin Calcium da ke tai...

YADDA AKE HADA FARFESUN GANDA

 Farfesun Ganda


Kayan Hadi

  1. • Ganda
  2. •Attarugu
  3. •Albasa
  4. •Tumatiri
  5. • Nutmeg
  6. •Tafarnuwa
  7. •Maggi
  8. • kori
  9. • Kayan kamshi
  10. • Tukunyar dafa ganda (Pressure cooker)


YADDA AKE HADAWA
Bayan uwargida ta wanke ganda da ruwan kanwa domin cire karni, sai ta zuba a tukunyar dafa ganda domin samun farfesu mai laushi . Sai ta yayyanka albasa da tumatiri. Ta jajjaga attarugu daidai misali da tafarnuwa. Sai ta daka garin nutmeg ta zuba da maggi da kori da thyme. Sannan sai ta zuba ruwa daidai misali ta rufe. Sai ta jira ya nuna na tsawon awa daya. Sannan ta sauke.


Ana son cin wannan girkin da safe ko da dare. Wannan irin girki, shi ne, wanda ya fi dacewa da masu son rage kiba. Domin ganda ba ta dauke da sinadarin dada kiba, illa a ci kawai don dadi. Tafarnuwar da aka sanya a cikin girkin na rage mura da kuma kare wadansu cututtuka kamar su mura da sanyi da sauransu. Ana son a rika girka irin wannan girki ga maijego, domin samun ruwan nono da karin koshin lafiya.

Da fatan wannan girki zai sanya kunnen mai gida motsi. Ga dadi ga kuma arhar kayan girki. A sha lagwada lafiya.

Comments